Luke 4

Gwajin Yesu

1Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada, 2inda kwana arbaʼin, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.

3Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yǎ zama burodi.”

4Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ba da burodi kaɗai mutum zai rayu ba.’
M Sh 8.3


5Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. 6Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. 7Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”

8Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’
M Sh 6.13


9Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali, ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. 10Gama a rubuce yake:

“ ‘Zai umarci malaʼikunsa game da kai,
su kiyaye ka da kyau;
11za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’
Zab 91.1, 12


12Yesu ya amsa, ya ce, “An ce: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’
M Sh 6.16


13Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.

An Ƙi Yesu a Nazaret

14Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu koʼina a ƙauyuka. 15Ya yi ta koyarwa a majamiʼunsu, kowa kuwa ya yabe shi.

16Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majamiʼa kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yǎ yi karatu. 17Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta:

18“Ruhun Ubangiji yana kaina,
domin ya shafe ni,
in yi wa matalauta waʼazin bishara.
Ya aiko ni in yi shelar ʼyanci ga ʼyan kurkuku,
in kuma buɗe idanun makafi,
in ba da ʼyanci ga waɗanda aka danne.
19In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”
Ish 61.1 2


20Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majamiʼar, suka koma a kansa. 21Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”

22Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”

23Yesu ya ce musu, “Tabbatace, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”

24Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa.

25“Ina tabbatar muku a zamanin Eliya, akwai gwauraye da yawa a Israʼila, saʼad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani koʼina a ƙasar. 26Duk da haka, ba a aiki Eliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon. 27Akwai kuma mutane da yawa a Israʼila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake–sai Naʼaman mutumin Suriyan nan kaɗai.”

28Dukan mutanen da suke cikin majamiʼa suka fusata ƙwarai da jin wannan. 29Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa, 30amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.

Yesu Ya Fitar da Mugun Ruhu

31Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a Galili, a ranar Asabbaci kuma, ya fara koya wa mutane. 32Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko.

33A cikin majamiʼar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, 34“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai—Mai Tsarki na Allah!”

35Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, “Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!” Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, saʼan nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni.

36Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!” 37Labarinsa ya bazu koʼina a cikin ƙasar.

Yesu Ya Warkar da Mutane da Yawa

38Yesu ya fita daga majamiʼar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yǎ taimake ta. 39Sai ya sunkuya kusa da ita, ya kuma tsawata wa zazzaɓin, sai zazzaɓin ya sāke ta. Nan take ta tashi, ta yi musu hidima.

40Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su. 41Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi.
Ko kuwa Almasihu


42Da gari yana wayewa, sai Yesu ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa, da suka zo inda yake, sai suka yi ƙoƙari su hana shi barinsu. 43Amma ya ce, “Dole in yi waʼazin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.” 44Sai ya dinga yin waʼazi a majamiʼun Yahudiya.

Copyright information for HauSRK